Zuwa ga Ɗanbaiwa,


Wancan course da ka saya fa, ba shi zai kalli kansa ba.
Wancan post da ka yi bookmarking, ba shi zai aiwatar da kansa ba.
Wancan littafin da ka saya, ba shi zai karanci kansa ba.
Wancan video daka yi downloading, ilimin cikinsa yana nan a zaune har sai ka ɗauki mataki (action).
Wancan screenshots da ka tara na mota, gida, da kayan alatu na duniya, ka sani cewa ba hotuna ne za su saya maka su ba. Sai da kuɗi.
Su kuma kuɗi ba sa zuwa daga buri kaɗai; sai an haɗa da ilimi, aiki, himma, da ɗaukar mataki.
Ka tuna ya kai Ɗanbaiwa, himma ba ta ga rago.
Me kake yi a yau don gina gobenka, ya kai Ɗanbaiwa?
post-image
This page may contain third-party content, which is provided for information purposes only (not representations/warranties) and should not be considered as an endorsement of its views by Gate, nor as financial or professional advice. See Disclaimer for details.
  • Reward
  • Comment
  • Repost
  • Share
Comment
Add a comment
Add a comment
No comments
  • Pinned