YAKIN YAZO KARSHE INSHA ALLAH


Presiden Amerika Donald Trump ya bayyana cewa an kammala cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki da jamhuriyar Musulunci na Iran, sannan ya bada umarni Sojojin Amurka su janye daga toshewar da suka yiwa wani bangare na mashigin ruwan Hormuz
Trump ya bawa dakarun Sojin ruwan Amurka umarni su janye gaba daya daga mashigin ruwan Iran, su bar manyan jiragen dakon kaya na ruwa su wuce ta Iran domin a man fetur ya wuce ya wadaci duniya
Shugaban Amurka Donald Trump yana fitar da sanarwan nan sannan a bangaren Kasar Iran, majalisar tsaro na Kasar ta tabbatar da cimma yarjejeniyar; sai farashin danyen man fetur a Kasuwar duniya yayi mummunan faduwa, kamar yadda zaku gani a screenshot
Wannan labari ne mai farin ciki da na tashi da shi a safiyar yau Litinin, idan baku manta ba kafin a fara Yakin Amerika, Israel da Iran, anan Nigeria muna sayan farashin litar man fetur a kasa da Naira ₦800, amma bayan fara yakin sai da muka koma saya Naira ₦1,500, yakin sai da ya shafi duk Kasashen duniya
Wato yakin ya shafe mu kai tsaye, kuma mun cutu, an cutar da mu, wannan kadan ne daga sharrin yaki, domin yana shafar kowa, ko da kuwa wani bangare yayi nasara, sai ya cutu daga sharrin yaki
A dalilin yakin; Iran ta rasa manyan jami'anta na fararen hula da Soji, har da Shugaban addini na Kasar, an fasa mata cibiyoyin man fetur da masana'antu, tayi asaran kudade masu dumbin yawa
Haka ita ma Amerika ta rasa manyan jiragenta na biliyoyin Naira, ta rasa wasu Sojoji da sansanonin Sojinta dake yankin gabas ta tsakiya gabaki daya |ran ta ru$he su, wanda zata dauki lokaci mai tsawo kafin ta gyara, sannan Amerika ta rasa kimarta a idon duniya
A bangaren |srài|a ita ma ta fuskanci asaran wasu Sojojinta, Iran ta rusa cibiyoyin |srài|a na sarrafa man fetur da gas, da cibiyoyin sarrafa wutar lantarki da sansanonin Soji
Wadannan Kasashe guda uku kowace Kasa ta ji a jikinta, darajar Amurka da |sra'|a ya fadi Kasa warwas, yayin da daraja da izzar Iran ya tashi sama, Amurka da |srài|a tare da taimakon karnukan farautarsu na Kasashen Larabawa sun yiwa Iran taron dangi, amma Iran ita kadai ta tsaya ta gagara faduwa, wannan ya nuna karfin da Iran take da shi a duniya
Muna rokon Allah Ya kawo karshen duka yakukuwan da ake fama da su a duniya
Allah Ya bamu aminci da zaman lafiya a Kasar mu Nigeria
Lihat Asli
post-image
Halaman ini mungkin berisi konten pihak ketiga, yang disediakan untuk tujuan informasi saja (bukan pernyataan/jaminan) dan tidak boleh dianggap sebagai dukungan terhadap pandangannya oleh Gate, atau sebagai nasihat keuangan atau profesional. Lihat Penafian untuk detailnya.
  • Hadiah
  • Komentar
  • Posting ulang
  • Bagikan
Komentar
Tambahkan komentar
Tambahkan komentar
Tidak ada komentar
  • Disematkan