Ada wani abu da na lura da shi wanda da yawa ba ma ankara da shi.


Lokacin da ka fara yin consistency, sai wata murya a zuciyarka ta fara tura ka ka ɗora wa kanka abin da ya fi ƙarfinka. Saboda kana ganin kana cikin lokacinka, sai ka fara tunanin dole ka ninka ƙoƙarinka.
A gaskiya, kada ka saurari wannan muryar.
Misali, idan kullum kana yin 20–30 replies, kuma ka yi haka har tsawon wata ɗaya, sai zuciya ta ce maka:
"Ai za ka iya 100."
Ni dai shawarata ita ce, kada ka bi ta.
Domin abin da yakan faru shi ne, za ka fara 100 ɗin. Bayan wasu kwanaki ka gaji, ka daina 100 ɗin. Ba nan ka tsaya ba, har ma ka daina 20–30 ɗin da kake iya yi cikin sauƙi.
A ƙarshe sai ka zama burnt out 🥵, ka rasa kuzarin yin komai.
Na ga wannan yana faruwa sau da yawa, musamman a cikin matasa. Kuma ni kaina na taɓa faɗawa wannan tarkon.
Lihat Asli
Halaman ini mungkin berisi konten pihak ketiga, yang disediakan untuk tujuan informasi saja (bukan pernyataan/jaminan) dan tidak boleh dianggap sebagai dukungan terhadap pandangannya oleh Gate, atau sebagai nasihat keuangan atau profesional. Lihat Penafian untuk detailnya.
  • Hadiah
  • Komentar
  • Posting ulang
  • Bagikan
Komentar
Tambahkan komentar
Tambahkan komentar
Tidak ada komentar
  • Disematkan